ABNA24 : Shugaban mai shekaru 82, ya sha rantsuwa ne a gaban kotun tsarin mulkin kasar, a bikin da aka shirya tare da halartar shuwagannin kasashen Afrika 11.
An gudanar da bikin ne a cikin tsauraren matakai na tsaro, inda aka zuba ‘yan sanda da jami’an jandarma da kuma sojoji.
Shugaba Conde, dai ya samu damar tsayawa takara ne a karo na uku,bayan kwaskware kundin tsarin mulkin kasar ta hanyar mika shi a zaben raba gardama.
‘yan adawa na kasar dai sun kauracewa zaben, wanda ya bashi damar sake tsayawa takara a zaben shugabancin kasar na ranar 18 watan Oktoba da ya gabata.
342/